Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matukan Keke Napep Sun Gudanar Da Zanga Zanga A Maiduguri


Matukan a daidaita sahu ko KEKE NAPEP sun gudanar da zanga zanga a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, don nuna rashin amincewarsu da shirin dakatar da ayyukansu da gwamnatin jihar ke shirin yi.

A yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a zauren majalisar dokokin jihar Borno, gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa, nan da 20 ga Janairu 2020, gwamnati za ta takaita ayyukan masu KEKE NAPEP din a manyan hanyoyin jihar.

Gwamnan jihar Babagana Zulum ya kira taron gaggawa da shugabannin kungiyoyin matukan keken mai kafa uku don fayyace bayanai game da ayyukan nasu.

Ga cikakken rahoton cikin sauti, daga wakilin muryar Amurka, Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG