Gwamnatin Borno Ta Ja Kunnen Matasa Masu Farautar 'Yan Boko Haram

'Yan Civilian JTF, ko 'Yan Gora a Maiduguri

Gwamnatin ta yaba da ayyukan matasan na kawo saukin tashin hankali, amma ta ce ya kamata su kasance masu bin doka
Gwamnatin Jihar Borno ta ce zata kama ta hukumta duk wani matashin da aka samu yana cin zarafi ko satar kayan jama'a da sunan matasan nan masu aikin farautar 'yan Boko Haram a Jihar ta Borno.

Mataimakin gwamnan Jihar, Alhaji Zanna Umar Mustafa, shi ne yayi wannan gargadin a lokacin da ake bukin yaye wasu matasa su dubu daya wadanda gwamnatin jihar Borno ta horas take shirin turawa ma'aikatu dabam-dabam domin rage irin talaucin da aka ce yana daya daga cikin abubuwan dake haddasa rashin kwanciyar hankali a jihar.

Yce daga watan Nuwambar wannan shekarar, gwamnatin zata rika biyan duk wani matashin dake karkashin wannan shirin Naira dubu 15 a wata, yana mai fadin cewa matasan sun sadaukar da rayukansu domin maido da zaman lafiya, ita ma gwamnatin zata yi musu kokari.

Mataimakin gwamnan ya ce, “kune ku ka tsaya ku ka ce abubuwan dake faruwa a Borno sun isa haka, kuma Alhamdulillahi, abin ya faru haka a nan Maiduguri. Har yanzu akwai masu mugun halin nan a wasu sassan Borno, kada kuyi barci, ku neme su, domin nemanku suke yi. Duk wanda yayi abu mai kyau, zamu kyautata masa.”

Dangane da batun yin inshorar rayukan wadannan matasan dake wannan aiki mai tsananin hatsari, kwamishinan shari'a na Jihar Borno, Kaka Shehu Lawal, yace zasu gabatar da doka gaban majalisar dokokin jihar wadda zata tanadi irin diyyar da ya kamata a rika biyan iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko wadanda suka jikkata a dalilin kokarin da suke yi na farauto 'yan Boko Haram.

Kwararru da mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya su na yaba ma matasan a zaman wadanda suka kawo zaman lafiya cikin Maiduguri da kewaye, a bayan da suka sadaukar da rayukansu, suka dauki sanduna da adduna suka fara farautar 'yan Boko Haram. Ana kuma yaba musu a saboda akasari, in sun kama 'yan bindigar su na mika su ne hannun jami'an tsaro ba tare da sun kashe su ba.

Da yawa daga cikin wadannan matasan sun yi hasarar rayukansu a hannun 'yan Boko Haram, musamman a farkon fara wannan aiki nasu a cikin Maiduguri, daga baya kuma a wasu garuruwan dake kewaye da babban birnin.

Ga cikakken rahoton Haruna Dauda daga Maiduguri