Gwamnatin jihar Adamawa ta bukaci karin jami’an tsaro musamman sojoji domin dakile tashe-tashen hankulan da ake fuskanta masu nasaba da rikicin kabilanci ko addini, musamman a wasu kananan hukumomin jihar guda shida da suka hada da Numan, Lamurde, Guyuk,Demsa, Girei da kuma Mayo-Belwa.
Haka nan kuma gwamnatin jihar ta gana da shugabannin hukumomin tsaro da ke jihar don yiwa lamarin tufkar hanci.
Ko da na tuntube shi jim kadan da taron sirrin da aka gudanar, kwamishinan yada labaran jihar Adamawan Ahmad Sajo ya ce akwai abun dubawa game da irin tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yanzu.
“"A taron da muka yi, mun amince cewa zamu nemi karin sojoji don a baza su a wadannan wuraren. Mun kuma yi alkawarin kafa runduna ta musamman wato task force da zata kasance da soja, da 'yan sandan ko ta kwana, da jami'an tsaro ta farin kaya masu bindigogi.” inji Sajo
Zuwa yanzu akwai daruruwan yan gudun hijira da aka konawa kauyuka da ke cikin halin ban tausayi wadanda akasarinsu ke neman mafaka a wasu makarantu da ke cikin garin Mayo-Belwa.
Mallam Abdurrashid Abubakar shugaban daya daga cikin irin wadannan makarantu da yan gudun hijiran ke fakewa ya bayyana yadda ake ta samu karuwar ‘yan gudun hijira a makarantar inda har bullar cutar kyanda ta sa suka rufe makarantar.
“A kowace rana karuwa suke, yanzu a takaice muna da ‘yan gudun hijira sama da dubu biyu a makarantar.” inji Abubakar
To sai dai kuma shugaban karamar hukumar Mayo Belwa Hon.Muhammadu Bako yace suna nasu kokari to amma ya bukaci a kai musu tallafi.
Saurari rohoton
Your browser doesn’t support HTML5