Wata kotun kasar Amurka dai ta ba da umarnin a kama DCP Abba Kyari ne bisa zargin alakarasa da dan damfarar yanar gizo, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi a kafafen sada zumunta da ke baje kolin arzikin da ya mallaka.
Malamin ya bayyana hakan ne a wata hira da Muryar Amurka inda ya ce gwamnati za ta yi amfani da yarjejeniyar diflomasiyya tsakaninta da kasar Amurka, kuma dole ne a bi ka’idojin doka.
A cikin kwanakin baya-bayan nan ne wata kotu a Amurka ta ba da sanarwar neman DCP Abba Kyari ya je Amurka bisa zargin alaka da Hushpuppi ya ba Kyari cin hangi, zargin da yeke musantawa.
Hukumomin Najeriya sun dakatar da Kyari daga aikinsa, kuma tuni har an maye gurbinsa da DCP Tunji Disu.
Masana sha’anin tsaro dai sun bukaci a bi tsarin diflomasiyya wajen yin abin da ya kamata.