Sabanin yadda aka saba, inda bangarorin biyu su kan hadu a ofishin ma'aikatar ilimi ta tarayya ko kuma babban zauren taro na hukumar kula da jami'o'i ta kasa, NUC, an gudanar da taron ne a wani wuri domin kaucewa idanun 'yan jarida da masu sha'awar lamarin.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya jagoranci tawagar gwamnatin da ta hada da jami’an ma’aikatar kudi da hukumar albashi da ma’aikata da mambobin kwamitin Farfesa Nimi Briggs da aka kafa domin sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 tsakanin bangarorin biyu da dai sauransu.
Duk kokarin da ‘yan jarida suka yi don gano wurin da bangarorin biyu ke ganawar, ya ci tura.
Taron dai ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuduri aniyar magance manyan bukatun kungiyar ASUU, da su ka hada da tabbatar da tsarin bayyana gaskiya da adalci a jami’o’in, UTAS, a matsayin tsarin biyan kudi a jami’o’i, da biyan alawus na ilimi, da kuma biyan albashin malamai masu yajin aiki da aka dakatar tun Maris 2022.
Ana sa ran taron zai kawo karshen yajin aikin da ya addabi jami'o'in gwamnati da kuma sake mayar da inganta tsarin jami'o'i a Najeriya.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya yi tsokaci kan taron tun da farko, a ranar Talata, ya yi alkawarin cewa kungiyarsa za ta janye yajin aikin idan har aka biya wasu bukatu.
Ya ce tuni kwamitin sulhu ya cimma yarjejeniya da gwamnati na tabbatar da UTAS a matsayin tsarin biyan malamai da kuma dakatar da yajin aikin.