A shirin mu na nishadi bayan dogon hutun da aka dauka na watan Ramadana, wakiliyar DandalinVOA ta samu ganawa da Hamisu Lamido Iyantama na masana’antar Kannywood.
Jarumi mai shirya fina-finai na Iyantama Multimedia, akan batun wani kwamiti na hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, wajen lalubo hanyoyin inganta masan’antar ta Kannywood.
A kwanakin baya ne aka kafa wani kwamiti da zai fitar da sababbin hanyoyin abubuwan da suka shafi harkar fim domin shiga kasuwa irinta zamani, tare da kawar da dukkannin nakasu da ke hana cigaba a masana’antar.
Iyantama ya ce wannan kwamiti dai ya samo asali a wani yunkuri da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bukata, inda ya zamo yana mai shugabantar wannan kwamiti, duk da cewar bayan kaddamar da wannan kwamitin ya na tare da wasu kalubale daga fannin gwamnati.
Ya ce wani babban kalubale da kwamitin ya fuskanta dai akwai matsala ta kudi, inda ya ke cewa bayan gwamnati ta bukaci da a kafa wannan kwamiti, sai gwamnatin ta cire hannu, ta barsu da kansu. Kin fitar da kudin da gwamnati tayi domin tafiyar da kwamitin, ya sa wadanda suke cikin kwamitin suka dinga fitar da kudadensu domin tafiyar da kwamitin.
Ko da gwamnati ta manta da su sai da suka ga hankalin hukumar tace fina-finai inda suke ce mata tun da ta kafa kwamitin, ya kamata ta dauki dawainiyar kwamiti wajen bata hakkokinta na tafiyarta da ita ta hanyar basu kudaden da ya kamata don samun cigaba.
Iyantama ya bayyana cewa kwamitin ya duba batutuwan satar fasaha, da maganar inganta masana’antar tare da tafiyar da zamani wajen fitar da wata kafar ta kasuwanci fina-finai ta kafar internet, kamar yadda yake a sauran sassan duniya.
A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Barak Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5