Iyayen ‘yan matan 11 na ci gaba da nema taimakon al’umma a ciki da wajen Najeriya don ceto ‘ya’yansu daga hannun bata garin da suka ce lallai sai an biya su kudin fansa na naira miliyan 100 kafin su sake su.
Iyayen da suka hada da mata da maza su 22 ne suka yi wannan kiran a yayin sake jadada yanayin kuncin da suke ciki ga al’umma a ciki da wajen Najeriya, a game da ‘ya’yan su da suka rage a hannun ‘yan ta’adda a cikin daji tun bayan sace su a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021, daga kwalejin gwamnatin tarayya na birnin Yawuri dake jihar Kebbi.
Iyayen ‘yan makarantar na ganin cewa, gwamnati daga matakin jihar zuwa tarayya sun ki sauraron kukan su a game da matsalar da suke ciki, da su ka bayyana cewa, ko sun sayar da dukan abinda suka mallaka ba za su iya tara kudin fansa na Naira miliyan 100 da ‘yan ta’adda suka nema domin su sako yaransu ba.
A game da wannan yanayin da iyayen yaran ke ciki suka kafa gidauniya ta musamman don neman taimako daga al’umma a ciki da wajen Najeriya domin samun kudin da za su karbo daliban da ke cikin daji tare da ‘yan bindigan.
A hirar shi da Muryar Amurka. Mal. Salim Kaoje, shugaban kungiyar iyayen 22 da suke neman taimakon, ya bayyana cewa gwamnati ta cuce su kasancewar babu wani taimako ko maganganun kwantar da hankali daga matakin jiha da ma na tarayya.
Da ta ke tsokaci dangane da lamarin, kwararriya a fannin ilimi kuma ‘yar Najeriya mazauniyar kasar Amurka, Malama Hauwa Mustapha Babura, ta yi kira ga gwamnati da duk wanda yake da dama ko halin da zai iya taimakawa su bada gudummuwa domin yaran su dawo hannun iyayensu,
’Yan matan kwalejin Yawurin 11 dake tsare a can din dai da su ka shafe kusan watanni 19 tare da ‘yan ta’addan a cikin daji inda a halin yanzu rahotanni ke nuni da cewa an aurar da 3 zuwa 5 daga cikinsu har suna da ‘yaya.
Duk kokarin jin ta bakin gwamnati daga matakin jiha zuwa tarayya ya ci tura a yayin hada wannan rahoton.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5