KADUNA, NIGERIA - A ranar Lahadi ne dai 'yan-bindiga su ka shiga garuruwan Tsonje, Agban, Katanga da Kadarko da ke karamar hukumar Kaura a Kudancin Jihar Kaduna su ka kashe mutane da dama.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta tabbatar kashe mutane 34 ciki har da sojoji biyu, mutane bakwai kuma sun jikkata yayin aka kone gidaje sama da 200 da shaguna 32.
Duk korafin da wasu kan yi game da fitar da sunayen mutanen da ake kashewa da gwamnati ke yi, masani kan harkokin tsaro Dr. Yahuza Ahmed Getso ya ce hakan ba zai taba zama matsala ba.
Ku Duba Wannan Ma Jami’an Tsaron Najeriya Sun Tarwatsa Wasu ‘Yan Bindiga Da Suka Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Jihar NejaTuni dai ganin munin wannan hari ya sa majalissar malamai da limamai ta Jihar Kaduna jajantawa al'ummar tare da jawo hankali don neman mafita, kamar dai yadda babban sakataren majalissar Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya fada.
Duk lokacin da irin wannan hari ya auku gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i ya kan jajanta kamar dai yadda ya yi a lokacin kaddamar da rahoton tsaro a farkon wannan shekara.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dan-masanin birnin Gwari Alhaji Zubairu Abdurra'uf Idris ya ce, al'ummar birnin Gwari na bukata gwamnatin jihar Kaduna ta yi masu irin wannan sakon jaje da juyayi a kamar yadda ta ke yiwa sauran bangarori.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5