Hukumar alhazai ta jihar Kano ta ce shirye-shirye sunyi nisa wajen tunkarar aikin Hajjin bana dake karatowa.Tuni an je an kama gidajen Alhazai kuma Gwamnati har ta biya tallafin da ta saba biya kusan milyan 242.
Malam Abdu Yakubu sakataren zartarwa na hukumar Alhazan jihar Kano ne ya furta haka ga wakilin muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.
Yace a hannu guda kuma ana ci gaba da jan hankali ga maniyyata aikin Hajjin game da hanyoyin samun yin Hajji karbabbiya, masu harkar bita suna yi mako mako sailin na kuma ana yin ta kafofin yada labaru.
Yace hukumar na aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki domin kula da maniyyata su fiye da 5000,
.Baya da taron bita da Gwamnati, ke shiryawa maniyyata kowace shekara malamai na ci gaba da bada tasu gudurmawar domin ilimatar da Alhazai kan aikin Hajji.
Fiye da maniyyata dubu 70, ne ake sa ran zasu sauke farali daga Najeriya, a bana kuma hukumar kula da Alhazan Najeriya, na shirin fara jikilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki cikin watan Agusta mai zuwa.