Matsalar yin garkuwa da mutane a Najeriya domin neman kudin fansa a bu ne da ya ki ci ya ki cinyewa, musamman a arewacin kasar, inda ‘yan bindiga suka bullo da sabon salon yin awon gaba da 'yan makaranta kamar yadda muka gani da 'yan makarantar sakandaren Chibok, Dapchi, Kankara, Kagara, Jangebe.
Na baya-bayan nan a kwalejin koyar da dabarun noma da lamurran da suka shafi gandun daji ta gwamnatin tarayyya da ke jihar Kaduna.
Masu ruwa da tsaki a Najeriya dai na ta yin kokari wajen neman a kawo karshen matsalar rashin tsaro, lamarin da ke kara ta’zarra inda Sanata Ali Ndume, ya yi cikakken bayani a kan abun da ya ke nufi kan samar da tsaro da hadin gwiwar 'yan kasa.
Game da batun tsaron rayukan ‘yan kasa idan suka bada bayanan sirri a kan batagari da ba su amince da ayyukan su ba, Sanata Ndume yace idan wani abu ya samu mai bayar da bayani, to ya kamata a tuhumi hukumar da abin ya shafa.
A nasa bangare, masani a kan lamurran yau da kullum, Auwal Lawan Uba, ya bayyana na sa ra’ayi a kan batun ‘yan kasa su hada kai da gwamnati don samar da tsaro.
An shafe sama da shekaru goma ana yaki da matsalolin tsaro a yankunan arewa maso gabas da rikicin mayakan Boko Haram, arewa maso yamma da rikicin ‘yan bindiga dadi da dai sauran sassan Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdurrauf a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5