Gwamnan Kano Ya Ce Yara Fiye Da Miliyan Uku Ke Ragaita A Titunan Jihar

Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

A shekarar da ta gabata ne gwamnan Kano ya bayyana a Kaduna cewa akwai yara fiye da miliyan uku da suke ragaita a titunan jiharsa saboda haka ya dauki wasu matakan shawo kan lamarin kamar yadda ya bayyanawa Muryar Amurka a wata firar da ya yi

A cikin shekarar data gabata ne a wurin wani taro a Kaduna, gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai yara fiye da miliyan uku da suka kai mizanin shiga makaranta, amma suna ragaita a titunan jihar.

Galibin yaran dai almajirai ne da kuma marasa galihu wadanda ba sa zuwa makarantun tsangayu ko na zamani.

Bayan kimanin watanni biyar da bayyana wadancan alkaluma na yawan almajirai a Kano, ko wanne irin matakai gwamnati ke dauka daga wancan lokaci zuwa yanzu? Tambayar kenan da Muryar Amurka ta yiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan yaran.

A cewarsa yaran fiye da miliyan uku ba wai 'yan jihar Kano ne kawai ba. Yaran suna zuwa ne daga wasu jihohi har ma da wasu kasashen yammacin Afirka irin su Nijar da Chadi lamarin da ya zama wa jihar wata babbar matsala.

Kwamnatin Kano bata da kudin da zata gina azuzuwan da zasu dauki yaran amma gwamnan ya shawarci gwamnonin arewa a wata wasika da ya bayar cewa yakamata a hana yara masu shekarun zuwa makaranta zirga zirga daga wannan jiha zuwa waccan saboda yaran suna shiga Kano kullum. Idan kowace jiha ta hana yara zirga zirga daga wannan jiha zuwa waccen za'a magance lamarin, inji gwamnan.

Yanzu a cikin jihar Kano gwamnati na aika da malamai zuwa makarantun tsangaya su koyas da turanci da lissafi domin su iya yin jarabawar shiga makarantun sakandare da zara sun kammala karatun Kur'ani.

Dangane da sakacin da ake zargin wasu iyaye da yi gwamnan ya ce suna tattaunawa da masarautar Kano, da sarkin Kano da manyan malamai domin fito da wasu dokokin da zasu dubi al'amarin sosai ta fuskar addinin musulunci, musamman iyayen da suke da 'ya'ya da yawa da ba sa iya kula dasu.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Kano Akan Yaran Da Basa Makarantar Zamani - 3' 25"