Yau a Kano aka fara taron masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin dakile yawaitar shaye-shayen abubuwan da ke sa maye.
Ofishin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr Bukola Saraki ne ya shirya taron.
Taron kuma ya samu halartar shugabannijn al’uma, sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro da na masu yaki da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Ya kuma hado har da kungiyoyin sa kai, malamai da kuma dalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II shine ya wakilci mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar.
"Muna yaudarar kanmu ne kawai muddin ba ma fadawa kanmu gaskiya, matukar ba mu amince cewa, muna taka rawa wajen karuwar wannan matsala ba" Inji Sanusi.
Ya kara da cewa, “nawa a cikin ku suke ware albashi ga ‘yan banga kuma su sayi ababen maye su basu da nufin basu kariya daga ‘yan hamayya?”
Sarkin kara da cewa, shugabannin siyasa su ne babbar matsalar, tunda matasa sun gano cewa, ya fi riba ka zama dan banga domin tafiyar da rayuwa.
Manjo Janar Sale Maina da ke ba da shawara ga shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya ce lura da cewa akwai dangantaka tsakanin ta’ammali da miyagun kwayoyi da sha’anin tsaro da zaman lafiya a kasa, ya sa ofishin shugaban majalisar shirya wannan taro.
Shi kuwa da Dr Maikano Madaki na Jami’ar Bayero Kano, masanin halayyar dan Adam kuma kwararre kan binciken sha’anin ta’ammali da ababen sanya maye ya ce akwai bukatar mahalarta taron su yi nazari kan dokokin da suka shafi wannan fanni.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum