Yau Asabar 10 ga watan Febwairu, ake zaben kananan hukumomi a duk fadin jahar Kano. Za'a zabi shugabannin kananan hukumomi su 44, da kansiloli masu yawa.
Rahotanni daga jahar sun ce an makara wajen kai kayan zabe da malaman zabe. Wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, yace har sai bayan karfe daya na rana aka kai kayan zabe a wasu kananan hukumomin.
Amma babban abunda ya lura dashi a wuraren da ya zagaya, musamman a karamar hukumar Doguwa, ba zaben ake yi ba. Yace jami'ai suna baiwa matasa da aka tattaro katunan zabe da tawada, suna ta dangwalawa jam'iyya mai mulki a jahar.
Wakilin na Sashen Hausa yace, ana yin hakanne akan idon jami'an tsaro na 'Yansanda, wadanda bisa al'ada duk lokacin zabe, ake kawo su domin tabbatar da doka da oda.
Zuwa lokacin da muka zanta da Mahmud, bai kai ga jin ta bakin jami'an jahar don jin martanin su gameda abunda ya gani ba, da kuma makarar da aka yi na aikewa da kayan zabe kan lokaci.
Ga tattaunawar da muka yi.
Facebook Forum