Gwamnan Jihar Niger Ya Ziyarci Rafin Gora Inda Ambaliyan Ruwa Ta Yi Barna

Alhaji Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Niger

Matsalar ambaliyar ruwan matsala ce da aka dauki shekaru masu yawa ana fama da ita a jihohi daban daban na Nigeria, al’amarin dake haddasa hasarar dukiya mai dimbin yawa wasu lokutta har ma da rayukkan jama’a.

Jihar Neja dake kusa da gabar kogin Kwara ta sha samun wannan matsala ta ambaliyar ruwa dake haddasa hasarar amfanin gona mai dimbin yawa da muhallan jama’a.

A makon jiya kimanin matasa 10 ne hukumomin jihar Niger suka tabbatar da mutuwarsu tare da yin awon gaba da gidajen jama’a kimanin 300 a kauyen Rafingora dake karamar Hukumar Kontagora.

Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello da ya ziyarci garin ya ce har yanzu mutanen garin na cikin hadari bisa la'akari da abinda ya gani. A saboda haka ya ce zasu nemi tallafin gwamnatin tarayyar Nigeria domin tabbatar da an canza wa mutanen garin matsugunni .

Gwamnan ya ce ruwa ya cinye gidajen mutane idan ba’a tayar da wadanda suka saura a garin ba nan ba da jumawa ba su ma gidajensu zasu ruguje.

Yace mazauna garin suna cikin wani yanayi na tashin hankali a sakamakon hasarar muhallai dama uwa uba da kayayyakin abinci.

Wani mutum mai suna Yakubu Abdullahi cewa ya yi gidansa ya rushe, yanzu a cikin wata bukka yake kwana, matan sa guda uku kuma cikin daki guda suke kwana.

A halin yanzu Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar na ci gaba da tattara bayanai domin tantance asarar da ambaliyar ruwan ta haddasa kamar yadda Shugaban hukumar Alhaji Ibrahim Inga ya tabbatar.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Niger Ya Ziyarci Rafin Gora Inda Ambaliyan Ruka Ya Kashe Mutane 10, Ya Ruguje Gidaje 300 – 2’ 55