Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang Ya Ayyana Zaman Makoki Na Mako Guda

Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce kashe-kashen dake aukuwa a jihar ta'addanci ne tsantsa da wasu ke aikatawa akan jama'ar jihar, kuma dole a tinkare shi akan ayyukan ta'addanci, idan har ana so a yi nasarar dakatar da kisan mutane da barnata dukiyoyi.

PLATEAU, NIGERIA - A jawabinsa na sabuwar shekara, gwamnan na jahar Filato, Caleb Mutfwang yace a tsakanin watan Afrilu da Yuni na shekarar da ta gabata an kashe mutane dari hudu yayinda 'yan ta'addan suka kashe mutane fiye da dari da sittin a karshen shekarar.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce kuskure ne a alakanta harin da aka kai wa mutane a matsayin rikicin manoma da makiyaya.

Mu fade shi karara kisa ne na kare dangi."
Mutfwang

Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Mutfwang ya sanar da cewa, ya ware mako guda don zaman makoki a fadin jahar, tun daga ranar daya zuwa ranar takwas ga watan Janairun dubu biyu da ishirin da hudu.

Ya kuma bukaci al'ummar jihar su dukufa da yin addu'oin neman ķariya daga masu mugunta da suka tasar wa jama’ar jihar.

Da yake tsokaci kan lamarin, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya ce babbar matsalar ita ce yadda 'yan ta'addan ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka kora, suna kuma aikin hakar ma'adinai.

Sanatan ya ce kan haka ne takwaransa a Majalisar Dattawa, Simon Lalong ya bukaci a samar da hukuma da zata inganta yankin jihohin tsakiyar Najeriya.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta amince da tura karin dakaru a yankunan dake da matsalolin tsaron, don kawo karshensu.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar FIlato Caleb Mutfwang Ya Ware Mako Guda Don Yin Makoki .mp3