WASHINGTON, D.C. - A lokacin ziyarar, Zulum ya ce gwamnatinsa ta sanya dubban ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta a wani shiri da ake ci gaba da gudanarwa da nufin daukar ‘yan mata 500,000 a makarantun Firaimare na Gwamnati a fadin jihar.
Malala Yousafzai, ta zo Najeriya ne domin bikin cika shekaru 10 na jawabinta na farko da ta yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma bikin ranar Malala.
Kowace ranar 12 ga Yuli, Majalisar Dinkin Duniya na bikin ranar Malala don girmama Malala. Ranar kuma ta yi daidai da ranar haihuwarta, da ya dace a karrama irin rayuwar da ta yi tana fafutukar kwato 'yancin yara da mata.
Da ya halarci bikin na karrama Malala, Gwamna Zulum ya bayyana cewa ilimin yara mata shine babban abin da zai magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki mai dorewa. Ya ce ’yan matan da ba sa zuwa makaranta sun fi yawan yaran maza da ba su zuwa makaranta a fadin jihar Borno, shi ya sa gwamnatin jihar ke matukar sha’awar shigar da ‘ya’ya mata makarantu.
Da take nata jawabin, Malala ta bayyana kwarin gwiwa game da makomar ilimin 'ya'ya mata. Ta ce, “Su 'ya'ya mata suna da azama, sadaukarwa da kuma fatan samun makoma mai kyau.Ta ce ina murnar cika shekaru 10 na jawabin da na yi a Majalisar Dinkin Duniya kuma a yau Laraba ne nake bikin cika shekaru 26 na haihuwa.
Ta kara da cewa, “Tun daga jawabin da na yi a Majalisar Dinkin Duniya, na yi balaguro zuwa kasashe daban-daban na duniya, domin ina son kawo labaran wasu ‘yan mata. Jama’a sun ji labarina kuma sun fahimci yadda mace daya ta samu ilimi, don haka muna so mu tunatar da duniya cewa ta yi tunanin sauran miliyoyin ‘yan matan da ba su da damar yin karatu.”
Da take tsokaci game da saka hannun jari a fannin ilimi, Malala ta ce, “Muna bukatar dukkan shugabanni su zuba jari a fannin ilmin al’ummar da za su zo nan gaba, muna bukatar mu tabbatar da cewa muna saka hannun jari a hanyoyin kirkire-kirkire da na zamani domin samar da ingantaccen ilimi. Ilimi shi ne ginshikin gina kasa mai karfi, duniya mai karfi, da samun karfin tattalin arziki, zaman lafiya da kwanciyar hankali."
Uwargidan gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Umara Zulum, wacce ta tarbi tawagar a filin jirgin sama na Maiduguri, ita ma ta na cikin wadanda suka gana da gwamnan.
Saurari karin bayani a rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5