Vanessa Huguenin, mai magana da yawun ofishin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, ta fada a wani taron manema labarai cewa, "Mun firgita da girman hare-haren sama da na kasa da ake kaiwa a Jenin da ke yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, da kuma hare-hare ta sama a sansanin 'yan gudun hijira mai dimbin yawan jama'a." Ta kara da cewa akwai yara kanana uku a cikin wadanda aka kashe.
Sai dai ba ta amsa bukatar yin bayani kan shekarun wadanda abin ya shafa ba.
"An hana masu ba da agajin lafiya shiga sansanin 'yan gudun hijira na (Jenin), ciki har da isa ga mutanen da suka samu munanan raunuka," in ji kakakin WHO Christian Lindmeier, yayin da yake magana kan takunkumin da sojojin Isra'ila suka saka.
Kungiyar agajin kiwon lafiya ta MSF a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talatar da ta gabata, ta ce, jiragen yaki na soji sun lalata hanyoyin da ke kaiwa ga sansanin agajin, lamarin da ya sa ba zai yiwu motocin daukar marasa lafiya su kai ga wadanda suka sami rauni ba. "An tilastawa ma'aikatan jinya na Falasdinu yin tafiya a kafa, a wani yanki da ake ta harbin bindiga da jirage marasa matuka," in ji sanarwar.
Isra'ila ta ce makasudin aikin na ta shi ne ta tumbuke bangarorin Falasdinawa da Iran ke marawa baya, da ke da alhakin yawaitar hare-haren bindiga da bama-bamai da kuma yunkurin farko na yin rokoki.