Duk da irin saba alkawuran sulhu da wasu 'yan-bindiga su ka yi a baya, wasu malaman addini da masana na ganin cewa sulhun ne kawai hanya daya tilo da zai kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Wannan yawan nuna bukatar sulhun ne ya sa gwamnatin jahar Kaduna ta amince da sulhu tsakanin ta da 'yan bindiga a jihar, kuma tuni gwamna Uba Sani ya sanar da soke ayyukan 'yan sa kai, a matsayin matakin rangumar sulhu da 'yan-bindigan.
Gwamnatin tarayya ma ta yi na'am da wannan sulhun a yankin Birnin Gwari kamar yadda wakilin mai-baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro malam Nuhu Ribado ya tabbatar.
Sai dai kuma shugaban kwamitin da ya jagoranci wannan sulhun da 'yan-bindiga, sheik Musa Asadussunna ya ce ba nan take za a ga irin sauyin da ake fata ba. Ya ce "mu kaddara yau wani ne ya kamu da rashin lafiya, don ya sha magani ba shi yake nufin zai rabu da cutar nan take ba, dole ne za a dinga fuskantar 'yan matsaloli nan da can amma idan aka yi hakuri aka bi hanyoyin da suka dace, za a kai gaci.
Daga cikin abubuwan da masu adawa da sulhu da 'yan-bindiga suke kalo a mtsayin matsala, shine abubuwan da suka faru a baya, wanda gwamna Uba Sani ya ce an yafe komai.
Duk da fargabar tada alkawurran sulhun, jagoran 'yan-bindigan ya ce matsalar ta zo karshe.
A baya ma an yi irin wannan sulhun da 'yan bindiga a jihohin Zamfara, Katsina da Kebbi amma 'yan bindigan sun koma aikata munanan aiyyukan da suka saba. Lamarin da ya haifar da matsalar tsaron da jahohin yammacin arewa suke fama da su a Najeriya wanda har wa yau shi ne sular kafa kungiyoyin sa kai na tsaro a wasu jihohin.
Domin sauraron rahoton Isah Lawal Ikara, a latsa nan:
Your browser doesn’t support HTML5