Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa Nakasassu A Bikin Cikarsa Shekara Sittin da Haihuwa

Kekunan guragu da na dinki da injinan nika su ne gwamnan jihar Bauchi ya tallafawa nakasassun dasu.

Tallafin da gwamnan ya bada na cikin tsarin da ya shirya na bikin cika shekaru sittin a duniya kuma kamar yadda yace da kudinsa ya sayi kayan ba da kudin gwamnatin jihar ba.

A jawabinsa gwamnan yace tallafin shi ne aikin alheri na taimakawa wadanda Allah ya dora masu lallura a jikunansu.

Yace dalili ke nan da ya kaddamar da makarantar Islamiya a sunan iyayensa tare da rokon Allah ya basu ladar abun da shi yayi.

Gwamnan Bauchi M.A. Abubakar

A nata jawabin uwargidan gwamnan Hajiya Hadiza Abubakar ta gargadi wadanda suka anfana da tallafin su tabbatar sun yi anfani dasu domin inganta rayuwarsu. Ta kira wadanda suka samu tallafin abun yin sana'a su yi sana'ar.

Wadanda suka anfana daga tallafin ya samu sandar makafi da injin nika kuma kodayake shi makaho ne dansa zai dinga anfani da injin domin su samu kudin rayuwa da kuma daina yin bara.

Nakasassun sun yi murna tare da yiwa gwamnan addua da fatan alheri.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa Nakasassu A Bikin Cikarsa Shekara Sittin - 3' 14"