Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin Bauchi Ya Gurfanar da Sabon Jakada Kotu


Gwamnan JIhar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar
Gwamnan JIhar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar

Lauyan da ya shigar da kara a madadin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Bauchi Alhaji Sule Katagum, Barrister Usman Bappa Darazo yace Yusuf Maitama Tugga sabon jakadan da Buhari ya zaba daga Buachi, yayi anfani da kafar sada zumunta ya bata masa suna

Inji lauyan, suna bukatar kotu ta wanke Alhaji Audu Sule Katagum kana ta sa Tugga ya biya nera biliyan biyu, wato miliyan dubu dari biyu a matsayin diya.

Wai shi Alhaji Yusuf Maitama Tugga ya rubuta a shafinsa na Facebook inda yayi zargin cewa Audu Sule Katagun ya sace Musa Azare. Yana mai cewa shi Katagum ya sani cewa idan wani abu ya sami Musa Azare shi Katgum zasu kama. Ya cigaba da cewa wai Katagum ya ce Musa Azare ya sameshi a gidan gwamnatin Bauchi dake Abuja. Shi Musa Azaren yace yana jin tsoro amma daga baya sai aka ji labarin an sace shi.

Barrister Darazo yace bayanin da Yusuf Maitama Tugga yayi bata suna ne. Yace sun shigar da kara suna bukatan kotu tace abun da Tugga yayi bata suna ne. Ya ci mutuncin Sule Katagum saboda ya gayawa duniya yana sace mutane.

Bayan Tugga ya sa bayanin a Facebook har an samu sharhi ishirin da daya sakamakon abun da yayi. Wasu mutanen dake ganin mutuncin Audu Sule Katagum sun daina ganin mutuncinsa. Mutane da dama suna ganin laifin Sule Katagum, suna cewa yayi anfani da ikonsa ya musgunawa dan garinsu, ya cutar dashi.

A nashi bahasin lauyan dake kare Tugga Barrister Mustapha Tafarki yace suna nazarin karar da aka gabatar kuma sun shigar da nasu bukatun.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG