Gwamna Kashim Shettima Yayi Tur da Harin da Aka Kai Maiduguri

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno

Gwamnan ya mika jajensa ga wadanda harin bam ya shafa a kasuwar sayar da wayoyin salula ta Maiduguri jiya talata, yana mai alkawarin taimaka musu
Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno, yayi Allah wadarai da harin bam da aka kai kan wata kasuwar sayarda wayoyin hannu dake dab da gidan waya na Maiduguri, hedkwatar jihar, jiya talata da rana.

A cikin wata sanarwar da jami'in yada labarai na gwamnan, Isa Umar Gusau, ya bayar, gwamna Shettima ya bayyana jimamin wannan abu, tare da umurtar hukumomin kiwon lafiya na jihar da su yi duk abinda zasu iya na jinyar wadanda suka ji rauni a lokacin wannan harin.

Gwamnan ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

A wata hirar da yayi da Muryar Amurka, jami'in yada labarai na gwamnan, Isa Umar Gusau, yace da zarar gwamnan ya komo Maiduguri a yau laraba, zai gana da mukarrabansa da kuma jami'an tsaro domin nazarin irin tallafin da za a bayar ga al'ummar da abin ya shafa, da kuma matakan da za a iya dauka domin rigakafin irin wannan abu.

Gwamnan yana Abuja, yana ganawa da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaron kasa a lokacin da aka kai wannan harin na Maiduguri.

Game da batun ko zuwan tsohon gwamna Sanata Ali Modu Sherrif garin Maiduguri yana da nasaba da wannan harin bam da aka kai, Malam Isa Umar Gusau, yace binciken jami'an tsaro ne kawai zai iya bin diddfigin musabbabin wannan harin.

Harin dai shi ne na farko a cikin garin Maiduguri na kusan shekara guda.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Kashim Shettima ya Maida Martani Ga Harin Bam A Maiduguri - 3'23"