Dama dai a kwanakin baya an sami fashewar wasu abubuwa a yankin sabon Tasha dake garin Kaduna sannan aka gano wasu wadanda ba su fashe ba a yankin Rigasa.
Sai dai a wannan karon, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce rahoton sirri ne ya nuna yuwuwar dasa abubuwan fashewan da ya kamata al'ummar jahar Kaduna su sanya idanu.
Wasu dai na ganin wannan sanarwa na iya firgita al'uma, sai dai masanin harkokin tsaro Dafta Yahuza Ahmed Getso ya ce sanarwar ce mafita ga al'uma don su dauki mataki.
Ku Duba Wannan Ma Bam Ya Halaka Mutum Uku, Ya Raunata 19 A Jihar TarabaDama dai fitaccen malamin addinin Musulunci Dr. Ahmad Gumi ya ce fadakar da masu ikirarin addini su na kashe mutane kawai shine maganin wannan matsala baki daya.
A baya dai hare-haren 'yan-bindiga da sace-sacen mutane ne matsalolin tsaro a jahar Kaduna sai dai cikin wannan shekara fashewar abubuwa masu kama da bama-bamai na neman kutsowa domin ko kafin bom din da aka dasawa jirgin kasan Abuja-Kaduna, an kwakulo bama-baman da aka yi sa'a ba su fashe ba a wasu sassan jahar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5