Gwanatin Jihar Taraba Ta Mayarwa Hakimai Da Dagatai 4 Kujerun Su

Gwamnatin jihar Taraba ta ce sace-sacen jama’a domin neman kudin fansa a jihar na karuwa sakamakon fatattakar masu satar mutane da gwamnatocin arewa maso yamma Najeriya daga yankunansu da yanzu ke daukar mafaka a wasu yankunan.

Bayaga sace-sacen mutane da shanu, wadannan miyagun mutane sukan rubutawa al’umar Fulani wasikar neman su biya makudan kudade ta hanyar yi masu barazanar kai masu hari kan rugagensu inda suka kasa biyan kudaden.

Mataimakin gwamnan jihar Taraba Injiniya Haruna ne ya yi wannan furucin da yake amsa tambayoyi daga wakilin sashin Hausa Sanusi Adamu bayan ya sanar da maida hakimai da dagatai hudu daga cikin tara da aka dakatar daga aiki ranar ashirin da biyu ga watan Fabrairun wannan shekerar kujerarsu.

Matakin da ya ce ya biyo bayan sakamakon rahoton bincike da hukumomin tsaro suka mikawa gwamnati wanda ya wanke su daga zargin da aka yi masu a baya kan lamura da suka shafi harkokin tsaro na yankunansu.

Hakimai da dagatai da gwamnatin jihar Taraba ta maidawa kujerarsu sun hada da na Tella, Sengirde, Taka Dale.

Ga rahoton Sanusi Adamu daga Jalingo.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwanatin Jihar Taraba Ta Mayarwa Hakimai Da Dagatai 4 Kujerun Su