Wannan bala’in ne ya haifar da wasu matasa masu kishin jihohin nasu suka mike tsaye wajen shiga yakin sa kai ta hanyar taimakawa sojojin Najeriya wajen bankadowa tare da yakar ‘yan ta’addar na Boko Haram.
Sannan sun taka rawar gani sosai wajen zaftare karfin ‘yan ta’addar a yankunansu ta hanyar yi masu kamun kazar kuku suna mikawa jami’an tsaro.
Wannan ce ta sa aka dade ana tsinkaye da bada shawarwarin ya kamata matasan da ke aikin sa kai tare da sojoji game da yakar ‘yan boko haram cewa a rikidar da su su zama sojojin Najeriya don karfafa musu gwiwa.
To kuwa an fara hakan, domin kuwa yanzu haka wasu daga cikin ‘yan JTF din da aka fi sani da ‘yan kato da gora, sun sami shiga aikin soja.
Wadannan matasa da aka dauka kimanin guda 200 sun bayyana sanye da kayan sarki zuwa fadar gwamnatin jihar Borno don nuna godiyarsu da jaddada kasancewa a fafutukar kare kasarsu.
Gwamnan jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar Kashim Shettima ya nuna jin dadinsa tare da yiwa matasan jawabin karfafa gwiwa game da wannan dama da suka samu ta yiwa kasarsu aikin kare ta daga ta’addanci.
Wasu daga cikin matasan su ma sun bayyana jin dadinsu da kuma daaura damarar ci gaba da bada gudunmawarsu musamman ma a wannan lokacin da suka sami kwarin gwiwar Makala kakin aikin soja.
Wakilinmu Haruna Dauda Biu ya aiko mana da wannan rahoto na kasa.