Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Tattaunawa Da Tsagerun Niger Delta - Buhari


Mayakan kungiyar "Niger Delta Vigilante Group" ta Ateke Tom su na rawar daji cikin sansaninsu
Mayakan kungiyar "Niger Delta Vigilante Group" ta Ateke Tom su na rawar daji cikin sansaninsu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da kungiyar tsegerun Niger Delta Avengers domin ganin yadda za a kawo karshen hare-haren da su ke kaiwa akan bututai da kayayyakin mai.

Gwamnatin ta Najeriya ta ce ta na tattaunawa ne da tsegerun tare da shiga tsakanin jami’an tsaro da kamfanonin mai.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Jamus, Michael Zinner da ke shirin kammala aikinsa a kasar.

A farkon makon nan rahotnanni sun ruwaito ministan harkokin matsa da wasanni, Barrister Solomon Dalung ya na cewa ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabannin kungiyar Niger Delta Avengers.

Sai dai kungiyar ta musanta wannan ikrarin ministan.

Ko a baya, gwamnatin ta Najeriya ta nemi tsegerun da su zo su hau teburin tattaunawa, amma suka bijire.

Amma Buhari ya ce gwamnatinsa a shirye ta ke ta yi dubi kan wasu yarjeniyoyi da gwamnatocin baya suka kulla da tsegerun a karkashin shirin nan na afuwa da aka musu.

Malam Musa Zubairu, mai fashin baki ne kan harkokin tsaro, kuma Jummai Ali ta tambaye shi yadda ya ke kallon lamarin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG