Jami'ai a yankin sun zargi sojojin Habasha da kashe-kashe barkatai bayan sun fafata da mayakan al-Shabab a kauyen Wardinle, mai tazarar kilomita 30 yamma da garin Baidoa.
Wani dan Majalisar Dokokin Somaliya, mai suna Ibrahim Isak, wanda ya ziyarci kauyen jiya Litini ya gaya ma Muryar Amurka cewa shi da kansa ya kirga gwawarwaki 13 na farar hula da aka kashe nan take, yayin da wani mutum kuma ya mutu a hanyar kai shi asibiti. Ya ce dukkannin wadanda abin ya rutsa da su farar hula ne.
Wani tsohon Mataimakin Ministan tsaro wanda ke wakiltar yankin, ya ce ya tattauna da mutanen kauyen wadanda suka shaida masa cewa sojojin Habasha sun ratsa ta kauyen da daren ranar Lahadi kuma ga dukkan alamu suna farautar al-Shabab ne.
Daga karshe ya ce sojojin sun gaya ma mutanen kauyen cewa za su je inda su ke kyautata zaton mayakan al-Shabab na boye ne, mai tazarar kilomita uku daga wurin.