Mista Sam ya bukaci haka ne don magance rikicin gwamanti da ‘yan adawar kasar, da kuma kisan gillar da aka yiwa wani fitaccen mai sukar lamirin gwamnatin kasar Kem Ley a makon jiya.
Da yake magana da Muryar Amurka bayan gama jawabinsa ga ‘yan majalisun Turai, Rainsy yace, yana fatan Turai zata bi Kadin lamarin da yayi musu matashiya akai, da fatan hada shirin bada agaji ga kasar ta Kudu maso Gabashin Asia da ta maganar hakkin dan adam.
A yayin da ‘yan majalisar Kungiyar Tarayyar Turan ke da damar kada kuri’ar kakaba takunkumi game da lamurran da suka shafi kisan kai da na cin zarafin muhallai, yace suna tunanin dakatar da harkokin kudaden wadanda ake zargi da laifi.
Ya kara da cewa, ‘yan siyasar Turai na bayyana sha’awarsu ta ganin kasar ta Cambodia ta aiwatar da sahihin zaben nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, wanda yace haka ne kadai hanyar kawo canjin kwanciyar hanlaki da dimukuradiyya.