Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Tabbacin Kasashen Afirka Za Ta Yi Batun Sudan Ta Kudu a Taronsu Na 27


Shugabar Kungiyar Kungiyar Kasashen Afirka Ta AU, Nkosazana Dlamini Zuma
Shugabar Kungiyar Kungiyar Kasashen Afirka Ta AU, Nkosazana Dlamini Zuma

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka dake fama da matsalar mummunan rikicin da ke ta hallaka mutane a Sudan ta Kudu da karuwar rikicin adawa.

Yanzu haka dai suna ci gaba da taruwa a Kigali babban birnin Rwanda don yin taron kungiyar karo na 27 da aka fara a jiya Lahadi.

Wannan taron ya biyo bayan kazamin fadan da ake tsakanin gwamnati da ‘yan adawa da ya haddasa mutuwar mutane da dama. Haka kuma MDD ta yi gargadi kasar game da kar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a makon da ta ki yiwuwa.

Akalla mutane 300 aka kashe a birnin tsakanin 8 zuwa 11 ga watan Yulin nan da muke ciki kafin lafawar rikicin. A fadan da ake tsakanin magoya bayan Shugaba Salva Kiir da na tsohon shugaban kasar na farko Riek Machar.

Ba dai tabbacin ko kasashen Afirkar guda 53 na kungiyar zasu tattauna maganar sabuwar kasar ta Sudan ta Kudu ko a’a, wacce kuma bata cikin kasashen da suke membobin kungiyar ta AU.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce, rikici a matalauciyar kasar na dada ta’azzara wanda hakan ke dada haifar da fargabar rashin daidaiton kasar.

XS
SM
MD
LG