A rukunin A, akwai Najeriya, Ivory Coast, Guinea Bissau da kuma Equatorial Guinea.
Washington D.C. —
‘Yan wasan Guinea Bissau za su kara da masu masaukin baki Ivory Coast a wasan farko da zai bude gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Kasar ta Guinea-Bissau ta shawo kan matsalolinta a fagen kwallon kafa inda mafi akasarin ‘yan wasanta wadanda suke taka leda ne a nahiyar turai kuma ta halarci gasar ta sau hudu a jera a baya-bayan nan.
Guinea- Bissau na daga cikin kasashen Afirka da ba su taba lashe kofin gasar ba, amma kocinta Baciro Cande, ya ce yana da kwarin gwiwa za su kai ga gaci.
Kasar na rukunin A, wanda ke dauke da Najeriya, Ivory Coast da kuma Equatorial Guinea.
Wasan na yau za a kara ne a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, babban kasar kasar ta Ivory Coast.