Guguwar Florence Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum Biyar

Tsananin guguwar nan mai lakabin Florence ya ragu zuwa mataki mummunar guguwar da aka saba gani, bayan da ta afkawa jihar North Carolina, dauke da iska mai karfin gaske da kuma ruwa kamar da bakin kwarya, inda ta yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane biyar.

‘Yan sanda a birnin Wilmington, sunce wata mata da jaririn ‘danta sun mutu bayan da wata bishiya ta fada kan gidansu. Sannan kuma wata mata a karamar hukumar Perder dake jihar North Carolina, ta mutu sanadiyar bugun zuciya bayan da ta kira waya tana neman taimako, sai dai motar daukar marasa lafiya ta kasa zuwa gidan matar saboda bishiyoyin da suka fadi suka rufe hanyoyi.

Jami’ai sunce mutane biyu sun mutu karamar hukumar Lenoir. Wani mutum mai shekaru 78 ya mutu bayan da wutar lantarki ta ja shi, yayiin da yake kokarin hada wayar wutar lantarki, ya yin da iska kuma ta buge wani mutun ‘kasa har ya mutu lokacin da ya fita duba karensa.

Cibiyar Nazarin Mahaukaciyar Guguwa ta Kasa ta ce karfin guguwar Florence ya ragu zuwa karfin guguwa mai tsanani da aka saba gani …. Kuma yanzu haka tana tafiya sannu a hankali zuwa kudu maso gabashin jihar North Carolina, tana tafiyar kilomita 110 cikin sa’a.

An ceto daruruwan mutane yayin da ruwa ke da’da karuwa. A karamar hukumar Craven jami’ai sunce sun sami kiraye-kirayen waya na bukatar kai dauki sama da 150 domin su ceto mutane daga garin New Bern ‘din nan mai dinbin tarihi, saboda ruwa ya shiga gidajensu.