Gudun Bada Na Shan Ruwa Ke Sa Samari Rabuwa Da 'Yan Mata Gabanin Ramadan

A shirinmu na mata a wannan makon, yayin da ake kasa da wata guda na fara azumin watan Ramadan, wasu samari kamar kowacce shekara sun fara aran na kare domin gudun kada su kawo na shan ruwa.

Akan haka ne DandalinVOA ya ji ta bakin samari da ‘yan mata ko ya abin lamarinyake a bana, ko an sami sauyi. Hafiza Mohammad ta ce har yanzu lamarin bai canza ba, domin kuwa sun fara arcewa, ta kara da cewa haka nan kawai sai su fara kirkirar fadan da babu gaira babu dalili dan gudun kawo na shan ruwa

Ta ce samarin yanzu Allah ya hore musu rowa basa lia'akari da cewar kyauta na kara dankon soyayya, sun gwamace su kawo wani uzri.

Ita kuwa Atine Musa cewa ta yi nata samarinta na nan daram amma fa babu wani zancen kyauta, sai dai kawai suna zuwa suna cika ta da surutu, ta kara da cewa samarin yanzu sai dai budurwa ta dauki kyauta ta ba saurayi ya sa hannu ya karba.

Su kuwa samari ana ta kai wa yake ta hula, Muktar ya ce su kansu a yanzu suna ta kansu ne babu zancen wata kyauta, domin 'yan mata a cewarsa sun iya kirkirar hanyar da zau karba.

Ya ce saurayi a yanzu zai yi nasa ya kuma yi ta iyayensa sannan wata budurwa a can tana nan ta na jira abu ne da ba zai yiwuwa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Gudun Bada Na Shan Ruwa Ke Sa Samari Rabuwa Da 'Yan Mata Gabanin Ramadan