GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Yuni 07, 2018:Nazari Kan Tsarin Ciyar Da Yara A Makarantun Gwamnatin Najeriya

Grace Alheri Abdu

Ranar asabar za a cika shekaru biyu da kaddamar da shirin ciyar da kananan yara da abinci a makarantun gwamnati na Najeriya, da kawo yanzu ake gudanarwa a jihohi ishirin da hudu na kasar.

A cikin jawabinsa a bukin kaddamar da shirin, ranar alhamis tara ga watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha shida, mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, shirin na daya daga cikin shirye shirye inganta rayuwar al’umma guda biyar na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da aka warewa dala miliyan dubu dari biyar a kasafin kudin shekarar.

Bukin ya hada da gabatar da tsarin aiwatar da shirin, da kaddamar da wani littafi da aka rubuta da suna Global School Feeding Sourcebook, da zai kasance taswirar aiwatar da shirin, da kuma gabatar da kwamitin gudanarwa na kasa da zai sa ido a shirin da ake kira “Home Grown School Feeding Program” da turanci.

Wannan shirin dai ya sami asali ne daga wata cibiya mai zaman kanta ta dake birnin London mai hankoron inganta rayuwar kananan yara da ake kira PCD a takaice, da a halin yanzu take aiwatar da shirin a kasashen Afrika shida da suka hada da Ethiopia da Ghana da Kenya da Mali da yankin Zanzibar na kasar Tanzani da kuma Najeriya.

Banda samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara, wani burin shirin kuma shine inganta sa yara makaranta, da kuma kafafa masu guiwa su sa kai a karatu. Shirin kuma zai samar da ayyukan yi , da kuma taimakawa manoma da za a rika sayen kayan abinci daga gonakinsu.

Jihar Plato na daya daga cikin jihohin da ake gudanar da shirin. A cikin hirarsu da wakiliyarmu Zainab Babaji, Dr Sumayya Hamza mai ba gwamnan jihar shawarwari kan ayyukan gwamnatin tarayya, tayi Karin haske kan shirin.

Rahoton Zainab Babaji. Wakilinmu a jihar Kano, Mahmud Ibrahim Kwari ya kuma zaga wadansu makarantu da ake gudanar da shirin inda ya yi hira da yaran dake cin moriyar shirin.

Saurari Cikkaken Shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Tsarin Ciyar Da Yara Da Abinci A Makaranta-10:30"