Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Mayu 31, 2018: Tashin Hankali A Tsakanin Iyali, Kashi Na Uku


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Kafin muyi sallama da bakin da muka gayyata a wannan zauren domin nazari da neman hanyoyin shawo kan takurawa abokan zaman aure, wani lamari da yake kai ga kisa, yau zamu maida hankali kan kalubalai da suke fuskanta a yunkurin taimakawa wadanda suka sami kansu a wannan halin.

Yau ma muna tare da Barrister Maryam Ahmed wata lauya kuma ‘yar gwaggwarmayar kare hakin iyali, da Mallam Abba Bello, jami’in Kungiyar dake aikace aikacen kiwon lafiyar iyali, da kuma Dr, Haruna Yakubu na sashen kula da lafiyar kwakwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano duka a birnin Kano.

Malam Abba ya bayyanawa jagoran wannan tattaunawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari matakan da cibiyarsu ke dauka na shawo kan wannan lamarin.

Saurari Cikakken shirin.

Cin Zarafin Iyali Kashi Na Uku-10:20"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:21 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG