GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Yadda Zainab Aliyu Ta Sami Kanta Cikin Tsaka Mai Wuya-Mayu,02, 2019

Grace Alheri Abdu

Ranar Talata, talatin ga watan Afrilu, aka sami an sako Zainab Aliyu da gwamnatin kasar Saudiya ta kama bisa zargin safarar miyagun kwayoyi bayan samun jakka da sunanta dauke da Tramadol da aka haramta shigarwar kasar.

An bayyana cewa, nan da nan Mahaifin Zainab da kuma kakanta da aka bayyana a matsayin wani mai hali a Kano, suka shiga neman hukumomin Najeriya su sa baki a sako ta, kasancewa bata da masaniya a kan jakkar da aka samu da kwayar, aka kuma dace bayan kimanin watanni biyar aka sako ta.

Shirin Domin Iyali ya nemi sanin ainihin yadda Zainab ta sami kanta a wannan halin akasin rahotonnin da ake yayatawa a kafofin sadarwa cewa wani ya sa kwayar ne a jakkarta ba tare da saninta ba. Mohammad Ajiya mataimakin kwamandan hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi a tashar Mallam Aminu Kano ya yi cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru a hirarsu da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

yadda aka sa kwaya a jakkar Zainab-10:30"