Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Rahoton Korar Jami'in Soja Da Ya Yiwa 'Yar Gudun Hijira Fyade, Afrilu 11, 2019


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Wata kotun soja ta musamman da ta zauna a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, ta ragewa wani babban jami’in soji girma ta kuma kore shi daga aiki bayan samunshi da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekaru goma sha hudu fyade a Maiduguri inda aka tura shi aikin kare rayukan al’umma da kuma murkushe kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya.

Bisa ga bayanin, yarinyar ta tafi bayan gari neman itacen wuta ne tare da wadansu yara da suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijiran da ake kira Bakassi Camp, lokacin da babban hafsan sojan ya sa suka kwakkwanta ya ware yarinja ya shigar da ita jeji inda ya yi mata fyade.

Saurari cikakken bayanin a wannan shirin.

Hukumcin sojan da ya yiwa karamar yarinya fyade-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:43 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG