Moniepoint wanda ya soma harkokin samar da kayayyakin more rayuwa da taimakawa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi wajen biyan kudade a 2015, ya bunkasa har ya kai ga gudanar da harkokin banki na kashin kansa.
Tara kudaden na baya-bayan nan ya samu goyon baya daga masu zuba jari irinsu hukumomin raya kasa da kamfanin Lightrock mai mazauni a landan dake tallafawa kananan masana’antu da asusun zuba jarin kamfanin fasahar sadarwa na google da kamfanin Verod Capital mai bunkasa kamfanoni a matsayin sabbin masu zuba jari.
Majiyoyi dake kusa da hada-hadar sun ce sabon zuba jarin da aka zuba ya kimanta darajar moniepoint fiye da dala biliyan 1, inda ya bashi matsayin “Unicorn”-kalmar da kamfanonin fasaha ke amfani da ita wwajen kimanta kamfanin da karfin jarinsa ya haura dala biliyan guda.
Za’a yi amfani da sabon jarin ne wajen hanzarta bunkasar moniepoint a fadin Afrika tare da samar da hadaddiyar mahada ta kasuwanci.
“Wannan dandali zai kunshi harkoki irinsu biyan kudi ta na’ura da harkar banki da musayar kudaden ketare da bada rance da kuma samar da dabarun gudanar da kasuwanci, inda ta zama matattara daya mai warware matsalolin kasuwanci da dama,” a cewar Momiepoint.
Najeriya ce kasuwar fasahar hada-hadar kudi mafi saurin bunkasa a nahiyar Afrika, sakamakon dimbin jama’ar da take dasu da suka haura mutum milyan 200, da kuma dimbin wadanda basu da damar samun hada-hadar kudi irin na bankuna.
A watan Agustan bara ne Moniepoint ya fara gudanar da harkokin banki na kashin kai.
Kamfanin fasahar hada-hadar kudin yace ya gudanar da harkoki fiye da sau milyan 800, da darajarsu a wata guda ta zarta dala biliyan 17.
-Reuters