Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ziyarci hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya, MDD, dake Abuja, babban birnin tarayya, inda harin bam da aka kai da mota ya kashe mutane akalla 19.
A yau asabar shugaba Jonathan ya mika ta’aziyya ga babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, dangane da wannan abinda ya kira hari na ragwanci. Yace gwamnatinsa tana kokarin kashe wutar ta’addanci, yana mai cewa zata kuma yi aiki da MDD tare da wasu shugabannin duniya domin maida martani ga harin.
Gwamnatin ta dauki karin matakan tsaro yau asabar a Abuja, inda sojoji suek binciken motoci tare da yin sintiri a kewayen ginin da ya lalace.
Hukumomi sun ce adadin wadanda suka mutu yana iya karuwa a yayin da asibitoci ke jinyar mutane akalla 60 da suak ji rauni a tashin bam din. Mutane kimanin 400 ne suke aiki a wannan gini na MDD dake Abuja, ginin dake dauke da hukumomi 26 na agaji da na ayyukan raya kasa.
Shaidu sun ce wata mota ta kutsa ta wuce shingaye biyu na shiga ofishin ta kuma yi bindiga a ciki, da misalin hantsi agogon kasar.
Wani mutumin da yace wai shi kakakin kungiyar Boko Haram ne yace sune suka kai harin. Mutumin ya fadawa wakilinmu a Najeriya cewa wannan mafari ne kawai. A cewar wannan mutumin, an kai wannan harin ne domin maida martanin karin sojojin da aka girka a Maidugurin Jihar Borno na arewa maso gabashin kasar inda wannan kungiya ta fi karfi.
Sai dai ba a san abinda ya hada ofishin MDD da girka sojojin da aka yi a Maiduguri ba.