Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Hannun Wani Na Kusa Da Al Qaida Aka Kai Harin Abuja


Wani sashen ginin MDD a Abuja bayan harin kunar bakin waken ranar Jumma'a
Wani sashen ginin MDD a Abuja bayan harin kunar bakin waken ranar Jumma'a

Hukumomin Najeriya sun ce Mamman Nur na Kungiyar Boko Haram ne ya tsara harin Abuja

Hukumomin Najeriya sun ce wani mutum mai alaka da kungiyar al-Qaida ne ya taimaka aka shirya harin bom din da aka kaiwa helkwatar MDD a Abuja a makon jiya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23.

Hukumar 'yan sandan ciki ta kasar Najeriya SSS ta fada a yau laraba cewa Maman Nur, dan kungiyar Boko Haram, shi ne ya tsara kai harin tare da wasu mutum biyu da ake zargi, wadanda su an kama su.

Sanarwar ta fada cewa kwanan nan Maman Nur ya koma daga kasar Somaliya inda ‘yan al-Qaida su ka taimakawa kungiyar al-Shabab ta yaki gwamnatin kasar.

Maman Nur bai shiga hannu ba har yanzu. Hukumomin Najeriya ba su bayyanawa jama’a mutanen biyu da suka kama ba amma sun ce ‘yan Boko Haram ne kuma sun yi muhimman bayanai.

Ranar Jumma’ar da ta gabata wani dan harin kunar bakin wake ya fasa wata motar boma-bomai a cikin ginin MDD a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, harin ya raunata mutane fiye da tamanin bayan 23 da suka mutu.

Wani mutumin da ya cewa Muryar Amurka shi dan Boko Haram ne, ya fada cewa kungiyar ce ta kai harin.

An sha dorawa Boko Haram laifin tashe-tashen boma-bomai da harbe-harben manyan shugabanni a arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma jahar Borno. Haka kuma kungiyar ce ta dauki alhakin kai hare-haren watan yuni a helkwatar 'yan sandan Najeriya ta kasa da ke Abuja.

Kungiyar so ta ke yi a kasa tsarin Shari'ar Islama a yawancin jahohin Najeriya.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawarin habaka tsaro tare da ganin bayan ta'addanci a kasar.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya na magana da 'yan jarida a Abuja bayan harin kunar bakin waken ranar Jumma'a
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya na magana da 'yan jarida a Abuja bayan harin kunar bakin waken ranar Jumma'a

XS
SM
MD
LG