Wata kungiyar Musulmi mai ra’ayin rikau a Nigeria, boko haram ta kai wani harin da aka boye bama bamai cikin mota daya kashe akalla mutane goma sha takwas a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria.
To amma direkta mai kula da aiyukan gaggawa a ma'akatar bada agaji, Air Commodore Bankole ya tabbatarwa wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda cewa mutane goma sha sidda ne suka mutu, mutane sittin da biyu kuma suka ji rauni.
Shedun gani da ido sunce wata mota ce ta kutsa kofofi shiga ofishin har guda biyu tayi bindiga a cikin harabar ginin kafin sha biyun ranar jiya juma’a. Bayan an kai harin, wani mai magana da yawun kungiyar Boko Haram ya buga wa wakilin sashen Hausa wayan tarho, yayi ikirarin cewa kungiyarsa ce keda alhakin kai harin. Harma yayi kashedin cewa wannan harin somi tabi ne.
Shi wannan mutumin mai magana da yawun kungiyar, yace kungiyar ta kai harin ne domin nuna rashin amincewarta ga kasancewar sojoji a birnin Maiduguri jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria.
Ita dai wannan kungiya, a cikin yan watanin da suka shige an dora mata laifin kai hare hare. To amma harin na jiya juma'a, ta kai ne ba'a wuraren data saba kaiwa ba a arewa maso gabashin Nigeria. A wata sanarwar daya gabatar, shugaba Jonathan na Nigeria ya lashi takobin hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin aikata wannan ta'adanci.