Gwamnati ta sanar da cimma yarjejeniyar ne da misalin karfe 1 na dare a birni Kudus, bayan da majalisar zartarwar ta yi wata ganawar sama da sa’o’I 6 kuma bayan shawarwarin da Majalisar tsaro ta bayar a ranar Juma’a na tabbatar da yarjejeniyar.
Taron da ya samu halartan dukkan mambobin Majalisar zartarwar ya dan shiga ranar hutun Yahudawa, wanda ke farawa baya rufe ayyukan a ranar Juma’a. A wannan ranar hutun, gwamnatin na rufe dukkan ayyuka, illa batutuwa na gaggawa da suka shafi rayuwa ko mutuwa, lamarin dake tabbatar da muhimmancin cimma wannan yarjejeniya.
Gobe Lahadi ne dai wannan yarjejeniyar zata fara aiki, zata kuma hada da dakatar da yakin tsawon makwanni uku da kuma sako gomman mutane da ake garkuwa da su da kuma sako Falasdinawa dake tsare a gidan yari.
Ma’aikatar shari’ar Isra’ila ta fada a ranar Asabar cewa za a sake fursinoni 737 da mutanen da ake tsare da su a matsayin wani bangare na Shirin tsagaita bude wuta da kuma sake mutanen da ake garkuwa da su.
Ma’aikatar Fursin ta Isra’ila ta fada a ranar Juma’a cewa tana daukar matakan hana wuce gona da iri wurin murna a lokacin da za a saki fursinonin Falasdinawan a wani bangaren yarjejeniyar tsagaita wuta.