Jiya Alhamis, Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da matakan sojin da Isira’ila take dauka a Gaza, ya na mai ayyana matsalar jinkai da ake fama da ita a wurin, “mai tsanani kuma abin kunya.”
“Babu yadda za mu taba amincewa da kai harin bam kan fararen hula,” a cewar Fafaroman a wani jawabin da wani hadiminsa ya gabatar a madadinsa.
Duk da cewa fafaroman, mai shekaru 88 a duniya, na nan a wurin gabatar da jawabin nasa, ya sa wani hadimin sa ne ya karanta jawabin, sabo da har yanzu yana kan murmurewa daga mura.
Wannan furucin wani bangare ne na jawabin sa ga jami’an jakadanci daga kasashen waje 180 a birnin Vatican.
Dandalin Mu Tattauna