Jami'ai sun ce Hamas ta amince da daftarin wata yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza tare da sakin mutane da dama da aka yi garkuwa da su.
Kasar Qatar ta bayyana cewa Isra'ila da kungiyar Hamas sun kai mataki mafi kusa na shirin kulla yarjejeniyar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya samu kwafin yarjejeniyar da aka tsara, sannan wani jami'in Masar da wani jami'in Hamas sun tabbatar da ingancinsa.
Wani jami'in Isra'ila ya ce an samu ci gaba, amma ana kokarin kammala matakan kulla yarjejeniyar.
Akwai bukatar a gabatar da daftarin yarjejeniyar ga Majalisar Ministocin Isra’ila don ta sahale shi.
Dukkanin jami'an uku da suka yi magana da AP sun yi ne bisa sharadin ba za a bayyana sunayensu ba.
Dandalin Mu Tattauna