Akalla mutane 41 suka rasa rayukansu a cikin wata mummunar gobarar da ta tashi a wani asibiti da ke kasar Koriya ta Kudu. Ana kuma fargabar cewa da kyar in yawan matattun ba zai karu ba a nan gaba.
Ko bayan wadanda suka rasa rayukansu, har ila yau akwai mutane kamar 70 da suka ji rauni, 10 daga cikin wadanda suka jikkatan suna da raunukan kuna a jiki masu barazana ga rayuwarsu.
Ma’aikatan kashe gobara sun ce, wutar ta tashi ne daga wani dakin tiyata na asibitin Sejong dake garin Miryang mai tazarar km 300 daga Seoul babban birnin kasar. Rahotanni sun ce, kamar marasa lafiya 200 ne ke kwance a asibitin lokacin da al’amarin ya faru.
Shugaban Koriya ta Kudu Moon-Jae-in ya kira taron gaggawa da mukarrabansa don tabbatar da cewa an dauki duk matakan da suka dace don taimakawa wadanda gobarar ta shafa.