Gobara Ta Sake Lakume Gida 83 a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Sansanin 'Yan Gudun Hijira

Gobara ta sake afkawa sansanin ‘yan gudun hijira tare da lakume gidaje 83 a garin Maiduguri na jihar Borno. Lamarin da ya jefa ‘yan gudun hijirar cikin mawuyacin hali.

Yawancin ‘yan gudun hijirar dake zaune a sansanin sun fito ne daga karamar hukumar Marte, wacce har yanzu ke fama da rashin tsaro.

Hakan ya sa suke samun mafaka a kauyen Fariya tare da ‘ya ‘yansu da dabbobinsu, wanda yanzu haka gobarar ta lashe fiye da rabin sansanin.

Mukaddashin gwamnan jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, ya kai ziyara domin ganewa idonsa yanayin da ‘yan gudun hijirar ke ciki tare da kai masu tallafi.

Yanzu haka dai gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar samar da agajin gaggawa ta NEMA, da ta sake ginawa ‘yan gudun hijirar gidajensu.

Haka kuma an samar musu da kayayyakin abinci, kamar yadda Alhaji Usman ya bayyana.

Duk da yake ba a sami asarar rayuka ba, wasu ‘yan gudun hijirar sun fadawa Muryar Amurka cewa, babu abin da suka tsira da shi daga cikin gidajen na su.

Shugabar hukumar samar da agajin gaggawa ta ce yawan dafe-dafen abinci a kusa da dakuna, shi ne babban makasudin yawan samun tashin gobara a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Wannan lamarin ya sa hukumar ta ce za ta ci gaba da fadakar da al’umomin domin ganin an dakile aukuwar tashin gobara a nan gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Gobara Ta Sake Lakume Gida 83 a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Maiduguri- 3'44"