WASHINGTON, D.C. - Wani shaidan kamfanin dilallancin labarai na Reuters ya ce ya ga gawarwaki biyu da aka ciro daga baraguzan ginin da ya rufta da misalin karfe 11:00 na dare (2200 GMT) a ranar Laraba. Mutane da dama kuma sun makale, sannan masu ba da agajin gaggawa suna ta kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Ginin ya kunshi gidajen zaman jama'a da kuma shagunan kasuwanci a cikin unguwar Garki da ke cikin kwaryar birnin Abuja.
Wani dan kasuwa daga wani gini da ke makwabtaka, Yakubu Inuwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Mun taimaka wajen fitar da wasu mutane, biyu da ba sa numfashi. An kuma fitar da mutane fiye da 20 daga cikin baraguzai."
Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, inda ba'a tabbatar da bin ka'idoji da kyau kuma kayan gini ba su da inganci.
📍 Muna tafe da cikakken rahoto mai karin bayani