Gina Jami’o’i Masu Zaman Kansu A Arewacin Najeriya Kalubale Ne Ga Shugabanni

Cincirindon Dalibai

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kirkiro karin jami’o’i masu zaman kansu 8 da kungiyoyi daban daban da Majami’u ke mallaka.

Majalisar ta amince ne bisa shawarar da hukumar kula da jihohin Najeriya NUC ta bayar. Yawancin jami’o’in dai za a ginasu ne a kudancin Najeriya, banda guda Daya tal dake a jihar Kwara wadda ake kira Crown Hill.

Kungiyoyi ne da Majami’u suka mallaki jami’o’in. Yanzu dai akwai adadin Jami’o’i masu zaman kansu 69 a Najeriya, inda daukacin jihohin Arewa 19 jami’o’i masu zaman kansu guda 10 ne kacal.

Daraktan labaru na hukumar kula da jami’o’in Najeriya, Ibrahim Usman Yakasai, yace hukumar bata banbance wadanda suka je neman izinin gina Jami’a, fatan hukumar shine wadanda zasu iya su cika ka’ida su gina, domin a samu karin gurabe da daliban Najeriya zasu iya samu suna shiga jami’a.

A cewar wani dan Arewa Saminu Azare, wannan wani babban kalubale ne ga shugabannin Arewacin Najeriya, domin hakki ya rataya a wuyanzu na ganin sun yi duk abin da yakamata wajen samar da jami’o’i masu zaman kansu, don habaka harkar ilimi a Arewa.

Missalan Jami’o’i masu zaman kansu kalilan a Arewa sun hada da jami’ar Nile a Abuja da kuma Jami’ar Amurka dake Yola fadar jihar Adamawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Gina Jami’o’i Masu Zaman Kansu A Arewacin Najeriya Kalubale Ne Ga Shugabanni - 2'57"