Gidauniyar Indimi Foundation Ta Raba Kayan Azumi Ga Mabukata

Shugabar Gidauniyar Indimi Foundation Hajiya Amina Indimi

Albarkacin watan Ramadan gidauniyar Indimi Foundation dake jihar Borno, ta taimakawa ‘yan gudun hijira da gajiyayyu da tallafin kudade da kayayyakin abincin na miliyoyin Nairori.

Gidauniyar Indimi Foundation ta ce ta kashe Naira Miliyan 70 wajen sayo kayayyakin abincin da take rabawa, tana kuma raba kudade.

Gidaunaiyar ta ce sun ‘dauki wannan mataki ne domin taimakawa mutanen da suka tsinci kansu cikin wannan masifa, wadanda wasu lokuta kan sha wahala wajen samun abin da zasu saka a bakinsu.

Haka kuma Gidauniyar ta mayar da hankali ga mata da kananan yara da rikin ‘yan kungiyar Boko Haram ya ‘dai-‘daita.

Dayawa daga cikin ‘yan gudun hijirar da suka sami wannan tallafi na abinci da kudi sun nuna godiyarsu da jin dadinsu ga wannan taimako da kungiyar Indimi Foundation ta yi musu.

Da take zantawa da wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, Daraktar gidauniyar Hajiya Amina Indimi, ta ce Allah ne ya basu ikon kai taimakon zuwa sansanin ‘yan gudun hijira a wannan wata mai falala. Haka kuma ta ce zasu ci gaba da fita asibitoci da sansanin ‘yan gudun hijira domin isarwa da mabukata taimako.

Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Gidauniyar Indimi Foundation Ta Raba Kayan Azumi Ga Mabukata - 3'31"