Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Horas Da Mata Fiye Da 200 Domin Dogaro Da Kai


A wani yunkuri na magance rashin aikin yi dake cikin manyan matsaloli da suka yi wa Najeriya dabaibayi,yanzu haka hukumomi a jihar Taraba sun horas da mata fiye da 200 domin dogaro da kai.

Masana dai sun yi ittifakin cewa rashin aikin yin da ke tafiya kafada da kafada da talauci, ya fi yawaita a tsakanin matasa da mata, musamman a arewacin kasar.

Kamar yadda alkalummar hukumar samar da aikin yi a kasar NDE ke nunawa, kawo yanzu dubban matasa da mata ne ke zaman kashe wando a Najeriya, wanda hakan ke zama tubalin rashin samun zaman lafiya a cikin al’umma.

Hukumomi sun dade suna yunkurin magance wannan matsala, koda yake da alamun an fara samun nasara a wasu jihohi, kuma jihar Taraba dake arewa maso gabashin kasar na cikin wadanda suka soma samun nasara biyo bayan tashi tsaye da aka yi ta hanyar horas da mata da matasa.

Na baya bayan nan ma shine wani koyon sana’ar da aka horas da wasu matan aure fiye da 200 a Jalingo fadar jihar, da kuma tuni kwalliya ta soma biyan kudin sabulu.

Masana dai na ganin ba yadda za’a samu nasara muddin ba’a dauko daga matakin kananan hukumomi ba, batun da shugaban karamar hukumar Jalingo Abdul Nasiru Bobboji, ke cewa su a shirye suke.

Shima Galadiman Muri Tukur Abba Tukur, wanda ya halarci bikin yaye wadanda aka koyawa sana’ar yace ko ba komi yanzu a samu wasu kayayyakin da ada ake shigo da su daga waje.

Kullum dai gwamnatocin jihohi kan yi tutiyar cewa sun samar da ayyukan yi ga matasa batun da kakakin jam’iyar PDP a Taraba Alhaji Inuwa Bakari, ke cewa gwamnatinsu tayi rawar gani.

Masana dai sun yi ittifakin cewa rashin aikin yin da ke tafiya kafada da kafada da talauci, ya fi yawaita a tsakanin matasa da mata, musamman a arewacin kasar batun da suka ce dole a tashi tsaye don fidda dan duma daga kabewa.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG