Gidan Jiya: Ana Wahalar Mai a Kano

Wasu 'yan kasuwar bayan fage ko kuma "Black Market" suna sayar da mai a Najeriya

Takaddama tsakanin kwamitin katta-kwana na gwamnatin jihar Kano kan sha’anin albarkatun man fetur da kungiyar dillalan man da kuma takwararta ta masu motocin dakon albarkatun mai ta barke a jihar.

Lamarin ya dawo da layuka a gidajen mai a birnin da kewayen Kano da wasu sassa na jihar Jigawa baya ga farashin man da ya yi tashin gwauron zabi.

A ‘yan kwanakin nan ne aka shawo kan matsalar man na fetur a kusan duk fadin kasar musamman ma a arewaci lamarin da ya galabaitar da al’umar kasar.

Samun matsalar karancin man fetur a Najeriya ba sabon abu ne tun bayan da matatun man kasar suka kwashe wani tsawon lokaci ba tare da suna aiki ba.

Koda ya ke a ‘yan watannin na aka dawo da wasu daga cikin matatun man cikin hayyacinsu.

Domin jin takaddamar da ta kaure a Kano har ta haifar da wahalar man, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari da ya turo mana daga Kanon Dabo:

Your browser doesn’t support HTML5

Gidan Jiya: Ana Wahalar Mai a Kano- 2'29"