ACCRA, GHANA - Shugaban babban bankin ya kuma bayyana cewa, daga cikin yunkurin gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasar gwamnati za ta rage albashin ma’aikatan ta masu mukami da kuma bude iyakar kasar cikin sati biyu mai zuwa
A hirar su da Muryar Amurka, wadansu ‘yan garin kamar Hajia Samira tace idan dai ya rage albashin ma’aikatan gwamnati domin ya taimakawa al’umma duka ya kyauta, ta ce shinkafa ta yi tsada mai ya yi tsada sabulu wanka ya yi tsada sabulun wanki yayi tsada.
Wani shi kuma mai suna Aminu Na Ta Gwando ya ce idan mutum ya ce zai baka riga toh ka dubi rigar da ya saka, saboda gwamnati ta sha yin alkawari, amma ba’a gani a kasa, idan abinda gwamnati take fadi gaskiya ne yayi kyau. Amma matsalar shine kada su saka wannan kudin a banki kuma bankin su kwashe suna sayarwa a bayan gida, a hakan kwalliya ba ta biya kudin tsabulu ba.
Masani a harkar tattalin arziki mallam Hamza Adam Attijani ya ce zai daga kudin ruwa daga kaso 2% zuwa 17%, tun shekarar 2018 rabon kasar da daga kudin, gwamnatin tayi hakan ne saboda rancen da babban bankin kasar ke baiwa kananan bankuna zai ragu sosai, idan anyi hakan kuma, za’a samu karancin kudi a kananan bankuna wanda zai sa mutani su kasa cire kudi ta banki domin gudanar da sana’o’insu da suka tsaba.
Hakan zai sa cidi yayi daraja, batun rage albashin ma’aikatan gwamnatin da kashi 30 zai sa gwamnatin kasar Ghana ta samu wasu kudaden domin biyan bukatun kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hawa AbdulKarim:
Your browser doesn’t support HTML5